Bisa ga ikirari muhimman jaridun Ibrananci uku na Isra’ila “Ma’ariv, Ha’aretz da Yediot Aharonot”; bisa yi la’akari da yanayin Isra’ila a matsayin abin takaici kuma ba a samu wani gagarumin ci gaba ba wajen ruguza Hamas, sakin fursunoni ko kyautata ra’ayin jama’a.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: bayan fara aikin guguwar Al-Aqsa a ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, kafofin watsa labaru daban-daban na duniya suna kokarin ba da labarin abubuwan da suka faru a kasar Falasdinu da ta mamaye, kuma bayan da aka fara kai farmakin yau kusan kwanaki 100 na wannan aiki, an watsawa labarai masu cin karo da juna daga Wannan ƙasa ga duniya.
Dangane da haka, ana iya daukar binciken aikin jarida na hukuma da na harshen Ibrananci a matsayin mafita don fayyace yanayin kura na yakin Gaza da kuma kara fahimtar yanayin da mazauna Isra’ila ke ciki.
Haaretz: Netanyahu mutum ne wanda ya gaza kuma mayaudari
A daidai lokacin da aka shiga rana ta 100 na yakin zirin Gaza, jaridar “Haaretz” ta yaren Ibraniyawa ta rubuta a cikin wani rahoto da ta fitar tana sukar firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu: “Bayan tsawon kwanaki na yakin da ake yi a zirin Gaza, abun da ke gaban Majalisar zartaswa ta Isra’ila shine ya zamo ta dawo da fursunonin daga wannan yanki, koda kuwa zai zamo sai tsagaita wuta ko kuma an sakin dubban fursunonin Falasdinu.
Rahoton ya ci gaba da cewa: Yin wasa da kalmomi a kafafen yada labarai ba ya canza komai. A halin yanzu, an maye gurbin wa’adin rushewar Hamas da kwance damarar zirin Gaza. Netanyahu mutum da ya gazawa a jere a fagage daban-daban.
Har ila yau Haaretz ta jaddada cewa: Muna shaida kasancewar majalisar ministocin da ta gaza ba ta iya yin aiki komai ba a karkashin wanda ya gaza kuma mayaudari. Majalisar ministocin Isra’ila ba ta damu da mazauna wannan yanki ba.
Yediot Aharnot: Muna fuskantar yaki mara iyaka
Ita ma jaridar ‘Yediot Aharnot’ ta ‘yan sahayoniya ta ruwaito cewa: Isra’ila ta makale a cikin wani rami mai zurfi da ake kira yaki ba tare da hangen nesa ba. Ta wace hanya al’amura ke tafiya cikin inuwar gazawa wajen cimma manufofin yakin?
A cewar wannan jarida, a ranar 7 ga Oktoba, Isra’ila ta rufta a cikin rami mai zurfi kuma abunda ya hau kai shine yadda za a fita daga ciki? Fitowa daga wannan rami yana nufin dawo da mutanen da aka kama tare da sake gina matsugunan da aka lalata da kuma tabbatar da tsaron mazauna kudanci da arewa da kuma ‘yantar da sojojin ajiyar da kokarin kawo karshen yakin. Wanda Wannan ba ƙalubale ba ne mai sauƙi.
Yediot Aharnot ta ci gaba da cewa: A cikin watanni ukun da suka gabata, mun ji labarin yadda Hamas ta sha kashi, amma wadannan labarai ba gaskiya ba ne, kuma har yanzu akwai sauran rina a kaba na rusa Hamas. Fasa wani rami na Hamas baya nufin ruguza karfin sojan Hamas.
Ko da a ce “Yahya al-Sanwar” (shugaban Hamas a Gaza) ko “Mohammed al-Dhaif” (kwamandan bataliyoyin al-Qassam) ko duka biyun an kawar da su, sakamakon yakin ba zai canza ba, kuma za’a samu wanda zai maye gurbinsa.
Dangane da kisan fursunonin yahudawan sahyoniya na wajen yan gwagwagrmaya da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi, wannan kafar yada labarai ta dauki matakin abin kunya ga wannan gwamnati.
Maaiv: Netanyahu ya rasa matsayinsa
A wani bincike da cibiyar bincike ta Lazar ta yi wa jaridar Sahayoniyya Ma’ariv, kashi 53 cikin 100 na mahalarta taron sun amsa tambayar ko gwamnatin Isra’ila ta yi nasara ko kuma ta yi rashin nasara a yakin da ake yi da zirin Gaza.
Kashi 22% na mahalarta taron sun ce gwamnatin Isra’ila ta gaza a wannan yakin. Kashi takwas cikin dari sun ce an yi wa gwamnatin Isra’ila mummunan fatattaka a yakin. Kashi 9% na mahalarta taron sun ce gwamnatin Isra’ila ta samu gagarumar nasara. Kashi takwas na mahalarta wannan binciken sun ce ba su sani ba.
Wannan jarida ta rubuta cewa: Biyo bayan jin ci gaba (gwamnatin Isra’ila) a yakin Gaza da kuma tabarbarewar batun mayar da fursunonin yahudawan sahyoniya da ci gaba da yakin da ake yi a arewacin yankunan da ta mamaye, kamar yadda binciken ya nuna. Jam’iyyar Likud karkashin jagorancin Firayim Minista Benjamin Netanyahu ta yi rashin nasara tare da faduwa zuwa wani matakin da ba a taba gani ba; Ta yadda idan aka gudanar da zaben Knesset (Majalisar) a yanzu, za ta lashe ku
jeru 16 ne kawai daga cikin kujeru 120 na Knesset.
Source: ABNAHAUSA