Japanawa Na Ban Kwana Da Tsohon Firaministan Kasar Shinzo Abe.
A Japan a wannan Talata aka fara gudanar da jana’izar tsohon Firaministan kasar Shinzo Abe, wanda wani dan bindiga ya kashe a ranar Juma’a.
Bayanai sun ce ana gudunar da jana’izar cikin tsauraran matakan tsaro a wurin bautar mabiya addinin Buda da ke birnin Tokyo.
Iyalansa ne kadai da kuma wasu mutane kalilan aka amincewa su halarci jana’izar, sai dai al’ummar kasar sun yi dandazo a kan layi a wurin ibadar domin ban kwana da shi.
Ana ci gaba da tsare dan bindigan da ya yi sanadin rayuwar Shinzo Abe wanda tun da farko ya dauki alhakin kisan ba tare da yin nadama ba.
Kisan da dan bindigan ya yi wa Mista Abe ya bakanta ran ‘yan kasar ta Japan da ke daukar tsauraran matakai kan amfani ko mallakar bindiga.
READ MORE : Shugabannin Kasashen Rasha, Turkiyya Da Iran, Zasuyi Taro Kan Siriya A Tehran.
Kasashen duniya da dama sun bayyana alhini kan kisan mutumin da suka bayyana a matsayin babban abokin tafiya.
READ MORE : Biden ba zai iya magance kiyayyar da aka yi wa gwamnatin sahyoniya da tafiya guda ba.
READ MORE : Yadda ‘Yan ta’adda suka kula da mu inji Fasinjan Jirgin Abuja-Kaduna da ya kubuta.