Ma’aikatar bunkasa al’adu da kula da ayyukan bude a kasar Japan, ta sanya masallacin Shizuoka a matsayin daya daga cikin muhimamn wurare a kasar, wadanda masu zuwa yawon bude ido za su iya ziyartar wurin.
Wanann masallacin da ake kira da koren masallaci ko kuma Green Mosque, yana daga cikin wurare na musulmi wanda aka yi amfani da fasaha ta musamman wajen gininsa da ke daukar hankula matuka.
Akasarin musulmin da suke rayuwa a kasar Japan dai sun zo ne daga kasashe daban-daban, musamman kasashen larabawa da kuam kasashen gabashin Asia, gami da kadan daga cikin mutanen kasar wadanda suka karbi addinin muslunci.
Musulmi suna rayuwa a cikin ‘yanci na gudanar da dukkanin harkokinsu na addini ba tare da wata tsangwama ko cin zarafi, ko kuma nuna musu banbanci ba.
A wani labarin na daban hukomomi masu kula da wurare masu tsarki a kasar Iraki sun bayyana cewa mutane kimani miliyan 16 ne suka sami damar halartar juyayin 40 na shahadar Imam Husain (a) a birnin Karbala.
Bayanin ya ce mutanen sun fito daga kasar ta Iraki da kuma kasashen duniya daban-daban, sannan daga kasar Iran kadai mutane kimani dubu 90 suka sami halartar juyayin, bayan da hukukomin kasar Iraki suka takaita adadin zuwa dubu 60 kacal da farko.
A wani rahoton kuma jami’an tsaro na Hashd Alshaabi na kasar ta Iraki sun bayyana cewa an kammala juyayin arbi’an a kasar ba tare da fuskantar matsalolin tsaro ba .