Jamus; Takunkumi A Kan Iskar Gas Na Kasar Rasha Kamar Bawa Mutanen Jamus Goba Ne.
Ministan kwadago na kasar Jamus Hubertus Heil ya bayyana cewa bai kamata kasar Jamus da dakatar da sayen iskar gas daga kasar Jamus a lokaci guda ba, dolene a nisanci sayensa a hankali a hankali.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Heil ya fadawahas jaridar Funke na kasar Jamus a safiyar yau Lahadi. Ya kumakara da cewa dakatar da sayan iskar gas daga kasar Rasha kamar an bawa mutanen jamus goba ne sukasha. Don hakan zai kawo tsadakar kayakin da mutane ba zasuiya dauka ba. Zai jawo rashin aikin yi, da talauci da kuma aikata laifuffuka zasu karu.
Ministan ya kammala da cewa har yanzun kasar Jamus na fama da matsalolin tattalin arzikin da cutar Covid 19 tajawo. Don haka yakamara gwamnatin kasar Jamus ta yi a hankali har zuwa lokacinda kasar zata wadatu daga sayan iskar daga kasar Rasha amma ba yanzu ba.
READ MORE : Yamen; Kawancen Saudia Sun Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Budewa Juna Wuta.
Kasashen Jamus, Hungary, Netherlands da wasu da dama sun dogara da iskar gas nakasar Rasha don amfani da shi a gidaje, kamfanoni da kuma sauran bukatu.