Gabanin kada kuri’ar wannan karshen mako, an kama dukkan manyan abokan Navalny, yayin da wasu suka tsere daga kasar, tare da hana duk wani mai alaka da jam’iyyarsa shiga zaben ‘yan majalisu da na kananan hukumomi da aka shirya za a rufe da karfe 8:00 na daren wannan Lahadi.
A wani labarin na daban kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci shugaba Vladimir Putin na Rasha da ya saki abokin hamayyarsa na siyasa Alexei Navalny. Merkel dai ta yi wannan kira ne a lokacin da take ganawa da shugaba Putin a wannan Juma’a a birnin Moscow.
Mukarraban Merkel sun bayyana cewar, ba kuskure bane ziyarar shugabar Jamus mai barin gado zuwa Moscow a dai-dai lokacin da ake tunawa da zagayowar ranar da aka sanyawa Navalny guba.
A wani bangare na ganawar da aka yada a gidan talabijin, Merkel ta ce, ‘’Duk da cewar muna da sabani a tsakanin mu dan gane da wasu batutuwa, akawai bukatar mu tattauna da juna dan samar da mafita’’.
Shugabar gwamnatin ta Jamus ta kara cewa, ‘’za mu tattauna kan wasu batutuwa, ciki har da, halin da ake ciki a Afghanistan bayan ‘yan Taliban suka kwace mulkin kasar, sannan ta ce akwai bukatar ci gaba da tattaunawa tsanakin Rasha da Ukraine don warware sabanin da ke tsakaninsu.