Jam’iyar Adawa A Kasar Angol Ta yi Kira Da A Gudanar Da Sabon Zabe A Fadin Kasar.
Babbar Jam’iyar Adawa a kasar Angola na ci gaba da nuna rashin amincewarta da sakamakon saben shugaban kasa da aka gudanar a kasar, inda dan takarar jam’iya ta Unita Adalberto Costa Juniour ya kalubalance kotun kundun tsarin mulkin kasar da ya rusa sakamakon zaben ya sa a sake gudanar da wani zabe
Hukumar zabe ta kasar ta tabbatar dan takarar jam’iyar MPLA kuma shugaban kasar mai ci a yanzu a matsayin wanda ya lashed a kuri’u 124 yayin da abokin hamayyarsa na jam’iyar UNita ke da kaso 90,sakamakon da UNITA ta yi watsi da shi kuma take ci gaba da kalubalantarsa a a kotun kundin tsarin mulki.
READ MORE : Kasar Rasha ta Dakatar Da Fitar Da Iskar Gas zuwa kasashen Turai.
A ranar Alhamis da ta gabata ce masu sa ido kan yadda aka gudanar da zaben suka mika rahotonsu kan yadda zaben ya gudana, day an kunci kungiyoyi da ba na gwamnati ba guda 61 da kuma sauran kungiyoyin addinai, in da suka nuna cewa rashin buga sunayen masu zabe ya yi illa sosai game da gaskiyar yadda aka gudanar da zaben.