Gwamnatin Nijar ta ce ‘yan ta’adda dauke da makamai sun kai hari akan jami’an tsaron kasar da ke aiki akan iyakar Burkina Faso, inda suka kashe jandarmeri guda 8 da kuma raunata wasu 33, yayin da jami’an tsaron suka kashe 50 daga cikin ‘yan ta’addar.
Sanarwar ta ce jami’an tsaron sun kashe akalla mutane 50 daga cikin ‘yan ta’addar, yayin da su kuma suka jikkata jami’an tsaron guda 6 bayan 8 da suka rasa rayukansu.
Gwamnati ta ce rawar da Jandarmerin suka taka tare da taimakon da suka samu daga wasu abokan aikinsu na kasa da na kasashen duniya ta kasa da sama ya taimaka musu wajen samun nasara.
Sanarwar ta ce rundunar Jandermerin ta yi asarar motocinsu guda 5 tare da babbar mota guda, yayin da ake suke ci gaba da sintiri a yankin yanzu haka.
Garin Waraou na yankin Tillaberi mai fama da tashin hankalin wanda ke kusa da iyakar Mali da burkina Faso.
A wani labarin an daban shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya sake gabatar da bukatar yin afuwa ga masu dauke da makamai a kasar domin ganin sun sake komawa cikin al’umma domin gudanar da harkokin su na yau da kullum.
Yayin da yake jawabi ga jama’ar Makalondi dake Yankin Torodi kusa da iyakar Burkina Faso, shugaban yace koda yaushe kofar su a bude take domin karbar mutanen dake shirin watsi da wannan mummunar aikin kai hare hare suna kashe jama’a.
Bazoum yace muddin irin wadannan mutane suka yi watsi da ayyukan ta’addanci, suka kuma aje makaman su, gwamnati a shirye take ta tsugunar da su da kuma taimaka musu ta fuskar sana’a.
Shugaban ya shaidawa mutanen yankin cewar ba zai taba barin su ba, kuma zasu ci gaba da Nazari akan halin da suke ciki domin tabbatar da zaman lafiya kafin mayar damutane gidajen su.