Mahukunta a kasar Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar dakarun kasar 4 da fararen hula 5, yayin da kuma ‘yan bindiga akalla 40 a jiya sakamakon gurmurzun da aka yi tsakanin dakarun kasar da kuma ‘yan ta’adda a yankin yammacin kasar kusa da iyaka da Mali.
Rahotannin da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce ‘yan bindiga masu tarin yawa sun kai hari da misalin karfe 3 na ranar Lahadi a wani gari da ake kira Tchoma Bangou, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka kai daukin gaggawa don kare fararen hula daga ‘yan ta’addan.
A lokacin wannan hari ne ‘yan bindigar suka kashe fararen hula biyar da kuma dakarun gwamnati 4, to sai dai jajircewar da sojojin suka ta ba su damar hallaka ‘yan ta’adda akalla 40 a cewar sanarwar.
Haka zalika dakarun gwamnatin kasar ta jamhuriyyar Nijar sun gano wani wuri da ‘yan ta’addar ke amfani da shi don boye babura da makamai masu tarin yawa, da suka hada kirar AK47 da kuma ‘machine gun’ da wadanda ake amfani da su don harba makami mai linzami wato RPG7 da kuma wayoyin sadarwa kirar Motorola.
Tchoma Bangou dai gari ne da ke cikin gudumar Ouallam da ya yi kaurin suna sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda da ke shiga kasar daga Mali, inda a cikin watan janairun da ya gabata aka samu asarar fararen hula akalla 70.