Jami’an Tsaron Isra’ila Sun Kashe Wani dan Falesdinu a yankin Jenine.
Rahotanni daga Falasdinu na cewa wani matashi ya rasa ransa yayin wani farmaki da jami’an tsaron Isra’ila suka kai a kusa da yankin Jenine dake gabar yamma da kogin Jordan.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ita ma ta tabbatar da mutuwar matashin dan shekara 17 mai suna Mohamed Abou Salah.
Kafar yada labarai ta wafa a falasdinu ta ce matshin ya rasa ransa ne sakamakon harbin bindiga lokacin farmakin da jami’an tsaron Isra’ilar suka kai a yankin.
Tunda farko dai rahotanni daga yankin sun ce an yi ta dauki ba dadi tsakanin jami’an tsaron Isra’ila da kuma Falasdinawa dake zanga zangar adawa da ziyarar wani dan majalisar yahudawan sahayoni a unguwar Cheikh Jarrah dake gabashin birnin Qods.
Kuma jami’an tsaron na Isra’ila sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashen roba wajen tarwatsa masu zanga zanagar inda mutum 31 suka jikkata.