Jami’an tsaro sun kwace Sakatariyar APC ta Kasa.
Jami’an tsaro sun kwace sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja.
Akwai rahotannin da ke cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a matsayin shugaban kwamitin tsare-tsare na rikon kwarya na jam’iyyar APC.
An bayyana cewa gwamnan jihar Neja, Sani Bello ne zai karbi ragamar tafiyar da harkokin jam’iyyar.
Sai dai da yake mayar da martani ga rahoton sakataren kwamitin riko, Sanata John James Akpanudoedehe, ya ce babu wani sauyin shugabanci a jam’iyyar.
A halin da ake ciki, duk hanyoyin da suka hada sakatariyar da ke Wuse 2, sun kasance a toshe, wanda hakan ya sa aka dakatar da zirga-zirgar ababen hawa.
Cikakken bayani yana nan tafe….