Kamfanin dillancin labaran Mawazin News ya bayar da rahoton cewa, jami’an tsaro sun fara daukar tsauraran matakan tsaro a kasar Iraki domin tarukan arba’in da za a gudanar.
Rahoton ya ce, a yankin Bagdad jami’an tsaro suna sintiri a cikin gari da kuma cikin dazuzzuka domin tabbatar da cewa babu wasu ‘yan ta’adda da za su kawo barazana ta tsaroa yayin gudanar da tarukan Arba’in.
Baya ga haka kuam sauran yankuna musammanma biranan Karbala da kuma Najaf, tun bayan kammala taruka ashura har yanzu jami’an tsaro suna nan cikin shirin ko ta kwana.
Daga cikin matakan da ake dauka dai kula da layuka na wutar lantarki da kuma layukan butun gas, kamar yadda kuam ake sanya ido a kan dukkanin kai koma na jama’a.
Sannan kuma an kafa kamarori masu daukar hotunan bidiyo a dukkanin yankuna da titina na mayna birane musamman Karbala da Najaf.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran Al’ain ya bayar da rahoton cewa, kwamitin kula da masallacin manzon Allah (SAW) ya sanar da cewa, an dawo da karatun halqa da aka saba gudanarwa a masallacin mai alfarma.
A ranar laraba da ta gabata ce aka gudanar da lacca ta addini ta farko a masallacin manzo (SAW) tun bayan bullar cutar corona, inda aka dakatar da laccoci da sauran bayanai da aka saba yi an addini a cikin wannan masallaci, saboda dalilai na kiwon lafiya.
Sheikh Abdulrahman Al-sudais ne ya gabatar da laccar, wanda ya yi bayani kan muhimman abubuwan da suka rataya a kan musulmi su kiyaye musamman lokacin da aka samu bullar annoba irin wadda ta game duniya.
Tun daga lokacin da cutar ta bulla ne dai aka dakatar da karatun halqa da ake a cikin masallacin ma’aiki (SAW) wanda mutane suke yin karatun littafai a wajen malamai na fikihu da hadisi da kuma tafsiri da sauran bangarori na ilimi.