An damke wani jirgin ruwan kasar Turai ya shigo Najeriya yana kokarin satar danyen man fetur.
Kamfanin NNPC ya bayyana cewa bai san da wannan jirgi da aka damke ba kuma ba bada lasisin diban mai ba Direban jirgin bayan tattaunawa da Sojoji ya gudu kafin aka cim masa a kasar Equitorial Guinea.
Jami’an Sojin ruwan Najeriya sun damke wani jirgin ruwa, (MT) HEROIC IDUN, mallakin kamfanin Hunter Tankers AS dake Scandinavia, Norway yana kokarin satar danyan mai a Najeriya.
Jami’in tsare-tsare da shirye-shiryen hukumar, Saidu Garba, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Juma’a, rahoton Premium Times.
A cewarsa, jirgin ya shigo Najeriya ne kuma kai tsaye ya nufi rijiyar man Akpo ba tare da izinin kamfanin NNPC ba.
Hukumar ta bayyana cewa jirgin ruwan ya isa rijiyar man ne cikin daren 7 ga Agusta da niyyar satar mai amma jami’anta suka dakilesu.
Yace: “Sakamakon bincike, NNPC ya bayyana cewa ko kadan bata baiwa jirgin izinin diban danyen mai ba.” “Hakan yasa aka tuwa jami’an sojin ruwa na NNS GONGOLA washegari don bincikan abinda ya kai jirgin Akpo.”
“Matukin jirgin ya bayyana cewa lallai basu da izinin diban mai a wajen.”
Saidu Garba ya cigaba da cewa sakamakon haka suka umurci direban jirgin ya jira sai NNPC ya bashi izini, amma Direban ya kurewa jirginsa gudu kuma ya nufi kasar Sao Tome and Principe, riwayar TheCable.
A cewar sa, daga baya aka damke jirgin ruwan a kasar Equatorial Guinea bayan kure masa gudu.
Gwamnatin Buhari Ta Bayyana Biliyoyin da Ake ci Duk rana a Tallafin Man Fetur
A wani labarin kuwa, kwamitin da aka kafa a Majalisar wakilan tarayya domin bincike a kan tallafin man fetur ya fara aiki a birnin tarayya Abuja.
Gidan rediyon FRCN yace kwamitin na musamman ya fara yin zama da Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed a majalisa.
Da aka gayyaci Ministar a gaban kwamitin domin tayi karin haske, ta shaida cewa gwamnatin tarayya na biyan N283 a matsayin tallafi a duk litar mai.
Abin da Ministar ta ke nufi shi ne duk rana sai tallafin man fetur ya ci wa gwamnati N18.397bn.