Adadin masu zanga zangar goyon bayan Falasdinawa da aka kama a yayin wata zanga-zanga a Jami’ar Texas ta Amurka ya kai 34, a cewar hukumomi.
“Ya zuwa karfe 9 na dare, jami’an tsaro sun kama mutum 34 a harabar Jami’ar UT Austin biyo bayan zanga-zangar yau da aka gudanar,” a cewar wani sako da Ma’aikatar Tsaron Al’umma ta Texas ta wallafa a shafinta na X, wanda a baya ake kira Twitter, a ranar Laraba.
Daga cikin wadanda aka kama har da wani mai ɗaukar hoto na gidan talabijin din FOX 7, Austin wanda ke daukar hoton zanga-zangar daliban a harabar Jami’ar UT Austin.
Hotunan soshiyal midiya sun nuna yadda aka kwantar da mai ɗaukar hoton a ƙasa kana aka ɗaure masa hannayensa.
Daliban sun gudanar da wani tattaki ne domin neman jami’ar ta janye kanta daga ƙera makaman da ke da alaƙa da Isra’ila.
Masu zanga zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali bayan da dakarun Sashen Tsaron Al’umma na Texas suka kutsa kai cikin taron.
Tattakin wani bangare ne na zanga-zangar gama gari na nuna goyon baya ga Falasdinu inda aka buƙaci cibiyoyin ilimi su janye daga kamfanonin da ke kasuwanci da Isra’ila.
Sai dai Ma’aikatar Tsaron al’umma DPS ta ce tana mayar da martani ne bisa ga bukatar jami’ar da kuma Gwamna Greg Abbott.
DUBA NAN: Zulum Ya Amince Da Fitar Da Kudi Domin Tallafawa Ɗalibai
Abbott ya ce za a ci gaba da kamen har sai taron ya watse.