Jami’ai masu gabatar da kara a Belgium sun sanar da nasarar kame gomman mutane a wani samame da ‘yan sandan kasar suka kai da taimakon jami’ai na ‘yan sandan Tarayyar Turai a kasashe nahiyar 6 na kan masu fataucin miyagun kwayoyi na kasa da kasa.
Gungun masu safarar muggan kwayoyin da aka kai wa samamen sun shahara ne a harkar dillancin hodar ibilis daga Kudancin Amurka, kuma sun samu damar gudanar da bincike a kansu ne da taimakon wani kuste da aka wa wata wayarsu ta tafe- da- gidanka da suke amfani da ita a kungiyance.
Batun na baya bayan nan dai ya shafi wasu masu safarar muggan kwayoyi ne daga gabashinTurai da ke zaune a yankunan birnin Brussels da kuma wasu ‘yan kudancin Turai da ke kungiyar mafiar nan ta Limburg, wato wani lardi da ke iyaka da Netherlands da suka yi kaurin suna wajen samar da muggan kwayoyi.
Wannan kame da jami’ai sukayi dai na zuwa ne bayan da a farkon wannan wata wani babban alkali, Ignacio de la Serna ya yi kashedin cewa yanzu fa ‘yan sanda ba su da nasibin dakile barazanar masu safarar mugga kwayoyi.