Jagoran kiristocin, Atallah Hanna ya bayyana take-taken gwamnatin yahudawan Isra’ila da take dauka na keta alfarmar masallacin Quds da cewa, hakan yana a matsayin keta alfarmar dukkanin adinai ne na ubangiji da aka saukar daga sama, ba addinin muslucni kawai ba.
Saboda haka jagoran ya ce kiristoci da musulmi da ma yahudawa masu lamiri gami da sauran al’ummomin duniya masu kishin ‘yan adamtaka a sahu guda domin kalubalantar wannan mataki na yahudawan sahyoniya.
Atallah Hanna dai yana daga cikin jagororin mabiya addinin kirista wadanda suke yin sadaukarwa wajen al’ummar falastinu da wurare masu tsarki na muuslmi da kirista da suke a birnin Quds.
Ko a lokacin yakin da Isra’ila ta kaddamar a ‘yan watannin da suka gabata, jagoran kiristocin ya yi ta shirya taruka da jerin gwano domin nuna goyon baya ga al’ummar yankin zirin zirin Gaza, tare da la’antar zaluncin Isra’ila a kansu.
A wani labarin kuma kamfanin dilalncin labaran Falastinu ya bayar da rahoton cewa, a jiya daruruwan yahudawan sahyuniya ne tare da mara baya daga sojojin Isra’ila suka shiga cikin masallacin Annabi Ibrahim (AS) da ke birnin Khalil Falastinu tare da keta alfamar wannan masallaci.
Shugaban kwamitin masalalcin Sheikh Hifzi Abu Saninah ya bayyana cewa, yahudawan sun garkame masallacin Annabi Ibrahim ne tun daga lokacin faduwar rana a ranar Talta inda suka hana yin sallar magariba a cikin masalalcin, daga lokacin kuma har zuwa yau yahudawan suna cikin masallacin.
Yace yahudawan sun kutsa kai a cikin wannan masallaci ne tare da keta alfarmarsa, da sunan gudanar da bukukuwan idin yahudawa, wanda suke yi a kowace shekara a wannan lokaci, wada ake sa ran mai yiwa bayan kammala idin nasu su fice daga masallacin.
Tun a cikin shekara ta 1994 yahudawan suka fara yin wannan kutse a cikin masallacin Annabi Ibrahim da sunan gudanar da bukukuwan yahudawa na shekaras-shekara.
Birnin Khalil na gabar yamma da kogin Jordan ne, sannan kuma akwai matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna guda 400 a gefensa da gwamnatin Isr’ila ta gina, inda sojojin Isra’ila ke gadinsu dare da rana.