Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Dinbin Halartar Mutane A Tattakin 22 Bahman Alama Ce Ta Karfin Ƙasa
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kuma kara da cewa idan aka gudanar da zabuka masu kayatarwa, za a iya ganin karfin kasa da tsaron kasa ya tabbatar da cewa: Tare da halartar mutane a fagen da lura da karfin tsarin kasa za a kawar da barazanar makiya, saboda ikon kasa da karfi, Yana haifar da tsaron kasa.
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarta cewa: Jagoran juyin juya halin Musuluncin a wata ganawa da yayi a yau da kwamandoji da ma’aikatan sojojin sama da na sojojin kasar ya kira mubaya’ar da akayiwa Imam Khumaini a ranar 19 ga Bahman 1357 a matsayin “Mai hanzartarwa” na juyin juya halin Musulunci, bayanin irin rawar da kebantattu wadanda sukai hanzari wajen mubaya’ar ke takawa – a ma’anar kungiyoyi da jigogin da ke aiki tare da daidaito da jaruntaka da sanin lokacin ganewa da dacewar asali – sun yi aiki a lokacin da ya dace. Ya kara da cewa: Kebantattun ta hanyar aiwatar da hanzarin da ya dace sun dauki nauyi mai nauyi wajen samar abunda ake bukata don tabbatar da manufofin juyin juya halin Musulunci.
Har ila yau Ayatullah Khamenei ya dauki cewa duk yadda halartar al’umma yayi yawa a zaben ranar 11 ga watan Isfand a matsayin tabbacin tabbatar da ikon kasa da tsaron kasa sannan kuma ya jaddada cewa: cikin yardar Allah al’ummar kasar za su halarci tattaki na kasa da kasa na ranar 22 ga watan Bahman. sannan kuma ta hanyar kare juyin juya hali za su nuna biyayyarsu ga Imam Khumaini
Babban kwamandan rundunar ya dauki wannan lamari mai ban mamaki na mubaya’ar da wasu gungun abokan tafiya da sojojin sama suka yi wa Imam Khumaini a ranar 19 ga watan Bahman shekaru 46 da suka gabata a matsayin darasi maras iyaka, ya kuma kara da cewa: Sojojin sama, tare da sadaukar da kai da wannan aiki na gaskiya da jajircewa wajen shigansu gaba-gaba cikin juyin juya hali sun ciri tuta.
A cikin kwanakin suka biyo baya ta hanyar tinkarar harin da dakarun tsaron Shah suka kai a cibiyar sojojin sama da ke Tehran, ya sanya jama’a da matasa sun fito kan tituna cikin shaukin da sha’awa. Wanda ya zamo ta dalilin hakan cikin nasarar juyin juya halin Musulunci a ranar 22 ga Bahman sun taka muhimmiyar rawa ta “masu hanzarin na kawo dauki a Lokacin da ya dace”.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da samar jihadi na dogaro da kai a cikin sojojin sama ‘yan watanni kadan bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Irin wannan ruhin karfi da jajircewa da karfin ruhi ne ya sanya sojojin sama suka zama majagaba da kuma kara kaimi a cikin juyin juya halin Musulunci wajen samar da jihadi na dogaro da kai.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya lisafta sojojin sama na zamanin Tagut da cewa gaba daya suna hannun kuma karkashin ikon Amurkawa ta fuskar umarni da manufofi da kayan aiki, sannan ya kara da cewa: Masu imani da juyin juya hali tare da jihadi mai dogaro da kai sun canja sojojin sama daga mallakin Amurka kuma gaba daya suka zamo dakarun Iran, inda suka nuna jagorancinsu da ikon kawo sauyi.
Ya kira mallakar ginshikai masu hanzari da tsara abubuwa a matsayin ci gaba da bukatuwa na juyin juya hali da kuma yunkuri na al’umma masu girma da manufa sannan ya ce: Bisa la’akari da kwarewar tarihi, a sannu ahankali manya-manyan yunkurori suna yin rauni har ma suna komawa baya, wanda samuwar wadannan masu hanzarin yana hana wannan annoba aukuwa.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira wasu daga cikin abubuwan masu jan hankali na cikin gida na juyin juya halin Musulunci da suka hada da yaki da zalunci da azzalumai, tsayin daka wajen tunkarar masu cin zarafi na duniya, mai da hankali ga al’ummar duniya da makomar kasar, a lokaci guda kuma suna mai da hankali sosai kan ruhi da tarukan addini, a matsayin sababin ci gaban sabon girma da kuma maye gurbin wurare wadanda suka mutu, inda yace: Duk da wadannan abubuwan jan hankali, juyin juya halin Musulunci da kasa na bukatar masu hanzari don kada mu yi kasala da rauni a manyan ayyuka.
Ayatullah Khamenei ya dauki waɗannan keɓantattun Ginshikai a matsayin masu kara kaimi na hakika, ya kuma ce a cikin wani muhimmin batu: Ma’anar Keɓantattu ba suna ne kawai ba; A maimakon haka, su ne mutane ginshikoki masu yin aiki da tunani da ilimi da fahimta a cikin kowane nau’i na al’umma kuma suke gudanar da ayyukansu cikin karfi da jajircewa a kan lokaci ba tare da bin yanayi ba…
Za Mu Ci Gaba
Source: ABNAHAUSA