Abinda zai zo a kasa matanin sakon jagoran addini na jamhuriyar musulunci ta Iran Sayyid Ali Khamene’i ne inda yake yabawa ‘yan wasan wadanda suka wakilci jamhuriyar musulunci ta Iran musamman bangaren ‘yan wasa masu tawaya ma’ana nakasassu wadanda suma sun taka rawar gani sosai da sosan gaske.
Ga matanin sakon jagoran :
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Ina godiya matuka da kuma yin jinjina ga ‘yan wasan Iran da suka nuna kwazo a a gasar motsa jiki ta nakasassu ta duniya wadanda suka faranta ran ‘yan kasarsu ta hanyar samun lambobin yabo na zinariya.
Sayyid Ali Khamenei
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran Mawazin News ya bayar da rahoton cewa, an fara daukar tsauraran matakan tsaro a kasar Iraki domin tarukan arba’in da za a gudanar.
Rahoton ya ce, a yankin Bagdad jami’an tsaro suna sintiri a cikin gari da kuma cikin dazuzzuka domin tabbatar da cewa babu wasu ‘yan ta’adda da za su kawo barazana ta tsaroa yayin gudanar da tarukan Arba’in.
Baya ga haka kuam sauran yankuna musammanma biranan Karbala da kuma Najaf, tun bayan kammala taruka ashura har yanzu jami’an tsaro suna nan cikin shirin ko ta kwana.
Daga cikin matakan da ake dauka dai kula da layuka na wutar lantarki da kuma layukan butun gas, kamar yadda kuam ake sanya ido a kan dukkanin kai koma na jama’a.
Sannan kuma an kafa kamarori masu daukar hotunan bidiyo a dukkanin yankuna da titina na mayna birane musamman Karbala da Najaf.