Jagoran juyi na Iran ya amince da yin afuwahukunce-hukuncen da aka yanke wa wasu fursunoni.
A yayin zagayowar zagayowar lokacin nasarar juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya amince da yin afuwa tare da sassauta hukunce-hukuncen da aka yanke wa wasu fursunoni 3,388 da suka hada har da wadanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai.
Shafin yada labarai na ofishin jagora ya habarta cewa, A yayin zagayowar lokacin nasarar juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya amince da yin afuwa tare da sassauta hukunce-hukuncen da aka yanke wa wasu mutanen, domin murnan zagayowar wannan lokaci mai matukar muhimmanci ga al’ummar kasar.
Alkalin alkalan kasar ya ce, shi ne ya rubuta wata wasika zuwa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci inda ya gabatar da shawarar yin afuwa ko sassauta hukuncin da aka yanke na mutane 3,388, Wadanda hukumar shari’a ta ce sun cancanta, Ayatullah Khamenei ya amince da wannan shawara wajen aiwatar da sashe na 11 na sashe na 110 na kundin tsarin mulkin kasar.