A safiyar yau Alhamis 17 ga watan Agusta, mambobin majalisar koli ta kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun gana da jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran a Husainiyar Imam Komain Rh da ke birnin Tehran babban birnin kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, A safiyar yau Alhamis 17 ga watan Agusta, mambobin majalisar koli ta kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun gana da jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran a Husainiyar Imam Khumaini.
Kafin cutar ta COVID-19, mambobin majalisar koli ta kwamandojin IRGC da jami’anta sun gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a daidai lokacin da ake gudanar da taronsu na shekara-shekara; Taron na karshe da bangarorin biyu suka yi a watan Oktoban 2018 ya gudana ne a gaban tsohon kwamandan rundunar Quds ta IRGC, Laftanar-Janar Qassem Suleimani.
Source: ABNA