Jagoran ‘yan gwgwarmaya na Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya bayyana jajen sa ga al’ummar Iran dangane da harin ta’addanci da aka kai a haramin Sayyid Ahmad bin Musa (S.a) a Shahcheraq dake birnin Shiraz dake Iran din.
Kamar yadda yazo a rubutaccen sakon shehin malamin ya bayyana harin ta’addancin a matsayin abin takaici wanda makiya suka shirya domin cutar da al’ummar musulmi. da suka hada da mata da kananan yara
Jagoran ya kara da cewa wannan harin babu abinda zai kara illah kara tsanar wanda suka haddasa shi.
Sheikh Zakzaky ya kuma bayyana jajen sa ga Jagoranjuyin juya halin musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i, Iyalan wadanda lamarin ya shafa da kuma al’ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran gabadaya.
Sheikh Zakzaky ya kuma yi fatan samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka kuma ya lullube shahidan da aka samu da rahamar sa.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin a babban birnin tarayyar Najeriyar ma ake zaman dar dar sakamakon wani rahoto da da ofishin jakadancin amurka ya fitar inda yayi da’awar ya gano za’a kai wasu hare hare a Najeriyar musamman babban birnin tarayyar Abuja.
Rahoton da da dama daga ‘yan Najeriya suka karyata kuma suke kallon hakan a matsayin wata makarkashiya ta samar da rashin tsaro a kasar su.
Kamfanin daillancin labarai na LEGIT dai ya wallafa cewa shugaba muhammadu buhari na Najeriyar zai shiga zama na musamman da jamj’an tsaron kasar domin kokarin shawo kan matsalar.
Wannan rahoto na Amurka dai ya sanya mutane musamman mazauna babban birnin tarayyar Abuja cikin wani halin dar dar inda wasu daga cikin kamfanunuwa soma kulle kofofin su sakamakon rashin tabbas.
Wasu na kallon idan gwamnatin Najeriya vara yi da gaske ba kasashen ketare zasu hargitsa zaman lafiyar kasar domin cimma wasu manufofin su na siyasa da tattalin arziki.