A yayin tarukan tunawa da zagayowar ranar shahadar babban kwamandan rundunar qudus na Jamhuriyar musulunci ta Iran Jagora juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Ali Khamne’i ya bayyana Sulaimani a matsayin wani alamin samar da yaci ga raunana.
Jagoran ya bayyana farfado da fada da zalunci a matsayin babban abinda Janaral Kasim Sulaimani ya cimma a rayuwar sa.
Jagora Ali Khamne’i ya kuma bayyana cewa, Sulaimani ya taimaki dagar gwagarmaya domin shirin fada da Isra’ila gami da shirya fada da kama karyar kasashe masu girman kai irin su Amurka.
Jagoran ya kuma bayyana murkushe kungiyar ta’addanci ta Da’esh a matsayin wani babbar nasara da Sulaimanin ya cimma a lokacn rayuwar sa.
Ali Khamene’i ya kuma bayyana yadda Sulaimanin ya fatattaki ta’addanci da ‘yan ta’adda a kasashen Siriya da Iraqi ta hanyar amfani da zarfiyyar cikin gida wacce suke da ita a kasashen na Siriya da Iraqin.
Jagora yana wanna jawabin ne a lokacin da iyalai da makusantan Janaral Sulaimani suka ziyarce shi a gidan sa dake babban birnin Tehran.
A wajen taron kuma Jagoran na juyin juya halin musulunci na Iran ya yabwa sabon kwamandan rundunar qudus bisa kokarin sa tun lokacin da ya karbi shugabancin rundunar.
A 2 ga watan janairun shekarar 2020 ne dai gwamnatin Amurka karkashin umarnin shugaban Amurkan na wancan lokacin Donald Trump suka kashe Janaral Kasim Sulaimani ta hanyar amfani da makami mai linzami a birnin baghdad na kasar Iraqi yayin da yake amsa gayyatar gwamnatin kasar Iraqin.
Kasashe da dama ciki har da kasashen Afirka suna gudanar da taron tunawa da shahadar Kasim Sulaimani wanda ke cika shekaru uku cur da yin shahada.
Kafafen yada labarai mabambanta sun rawaito labarin kisan Kasim Sulaimani da Amurka tayi bisa fahimtocin su mabambanta.
Tarukan tunawa da shahadar Kasim Sulaimani karo na 3 na cigaba da gudana a fadin duniya yayin da wasu da dama ya shigar musu duhu cewa, Shin wanene Kasim Sulaimani?