Jagora Sayyid Ali Khamene’i ya bayyana cewa tsomalen kasashen ketare, wadanda ba na asiya musamman amurka da kawayen ta shine babban dalilin da yake kawo cikas a lamurra tsaro da cigaban al’ummar nahiyar ta asiya, inda yayi kira fa kasashen asiyan da suyi koyi da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran a bangaren samar da tsaron kasa, dogaro da kai da kuma tafiyar da lamurra cikin tsari ba tare da barin bakin haure sunyi katsalandan a sabgogin tsaron kasa ba.
Jagora Ayatullah khamene’i ya bayyana hakan ne a wani taron yaye daliban doji da aka gidanar a birnin Tehran ranar lahadi 3 ga watar oktoban shekarar 2021.
Jagoran ya yabawa rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran bisa babban kokarin da sukeyi na tabbatar da tsro a kasar gami da kade duk wani hari na ciki da waje da makiya ke kawowa jamhuriyar musuluncin ta Iran.
Wannan kalaman na jagoran nazuwa ne bayan wani atisayen ba sani ba sabo da sojin kasa na Iran din suka gudanar a arewa maso yammacin kasar wanda ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian ya samu halarta a wani mataki na tauna tsakuwa domin aya taji tsoro gami da tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci Ta Iran ba zata lamuncin zaman sojoji yahudawan haramtacciyar kasar isra’ila a kusa da ita, wanda hakan ya biyo bayan lura da alakar dake tsakanin gwamnatin azarbejan (wacce makociyar Iran din ce) da haramtacciyar kasar ta isra’ila.
Jagora Ayatullah Khamene’i ya tabbatar da cewa sojojin kasashen yankin asiya sun isa su bada tsaro ga nahiyar kuma ya ja kunnen gwamnatcin kasashen yankin da kada su bada kafa ga sojojin yammacin turai a nahiyar domin kare manufofin su.
Jagoran ya bayyana cewa abinda ke faruwa yanzu hakan a arewa maso yammacin Iran wani mataki ne na hankali gami da lura domin tabbatar da tsaron nahiyar kuma ya bukaci sauran kasashen nahiyar suyi koyi da dakarun Iran din a wannan fage.