Jagora; Tsayin Daka Ne Yasa Al’ummar Iran Samun Galaba Kan Makiya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa al’ummar Iran, ta hanyar juriya sun yi nasarar karya laggon makiya.
Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da gungun jami’an shari’a a birnin Tehran a ranar tunawa da harin ta’addancin da ya kashe manyan jami’ai 74 ciki har da babban alkalin alkalan kasar Ayatullah Muhammad Beheshti a shekara ta 1981.
Jagoran ya bayyana bangaren shari’a a matsayin wani muhimmin ginshiki kuma mai tasiri a kasar, yana mai kira ga jami’anta da su ba da fifiko kan yaki da cin hanci da rashawa.
‘’tsayin daka da jajircewar al’ummar Iran a kodayaushe yana taimaka musu wajen samun galaba daga mawuyacin hali’’, Inji jagoran.
READ MORE : An Fara Tattaunawar Neman Ceto Yarjejeniyar Nukiliyar Iran A Doha.
Don haka a cewar jagoran Iran, za ta ci gaba da dogaro da Allah da koyarwa ta Al’Qur’a’ani mai tsari wanda shi ya kai ta ga samun wannan galaba duk da makircin makiya.
READ MORE : Sabon Fira Ministan Somaliya Ya Karbi Ragamar Jagorancin Kasar A Hukumance.
READ MORE : Bulgariya Ta Kori Jami’an Diflomasiyyar Rasha Guda 70 Daga Kasarta.