Jagora; Kowace Rana ranar Quds Ce Matukar Dai Yahudawa Suna Mamaye Da Masallacin Al-aqsa.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar wanda gidajen talabijin suka watsa kan ranar Quds ta duniya cewa, tsayin daka na Falastinawa yana samun karfinsa ne daga irin wadannan taruka masu albarka.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa matukar dai ‘yan mamaya yahudawan sahyoniya sun mamaye birnin Kudus, to dukkanin ranakun shekara ana daukar su a matsayin ranar Quds ta duniya, yana mai nuni da cewa matasan da suke gudanar da ayyukan sadaukarwa sun zama garkuwa ga Quds.
Ayatullah Khamenei ya yi ishara da cewa, a yau muna ganin America tana fama da shan kashi a fagagen siyasa, da kuma yadda yahudawan sahyoniya suke kai komo a fagen siyasa da na soja cikin sarkakiya na matsaloli.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa yunkurin jihadin da Falastinawa suka yi a yankunan arewaci da kudancin kasar a shekara ta 1948 yana nuni da cewa dukkanin Falastinu ta koma wata maraya ta gwagwarmaya.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce taken da masu fafutukar kare hakkin bil’adama a Turai suke ya tabbata cewa ba gaskiya ba ne, domin suna yin watsi da laifukan da yahudawan sahyoniya suke aikatawa kan yara da mata.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa karfin juriyar da suke da shi zai kawar da ‘yan ta’addar sahyoniyawan ta hanyar jihadin su.