Jagora; Adalci Ba shi Da Wani Ma’ana Ba Tare Da Taimako Da Kare Hakkokin Raunana Ba.
Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatullahi Imam Khamna’I ya fadi haka ne a alokacin da yake ganawa da limaman juma’a a fadin kasar , inda ya bayyana sallar juma’a a matsayin wata mahada mai muhimmanci sosai kuma wani aiki na musamman wajen nuna irin alfanu da tsarin musulunci yake da shi,
yace limamin juma’a shi ne kakakin juyin musulunci kuma yana daga cikin ayyukansa isar da ma’anoni ilimi da manufar hallita da ginshikin juyin musulunci da kuma amsa shibuhohu da harshen zamani , da kuma yin muamala ta iyaye ga kowa,
har ila yau ya nuna cewa akwai kurakurai da dama day a kamata mu yi kokari wajen ganin mun kawar da su , kuma a halin yanzu wasu abubuwa nauyinsu ya taya ne akan limaman juma’a wasu kuma yana kana hukumar gudanarwa da kula da sallar juma’a
Jagoran ya ci gaba da cewa muna goyon bayan Adalaci kuma mun daga tutarsa , sai dai tabbatar da Adalaci ba tare da Taimakon wadanda ake zalunta da raunanan ba bashi da wata Ma’ana
Daga karshe ya nuna cewa jamhuriyar Musulunci ta iran ba kawai ta kebance kanta da taken kiyaye Addini ba ne ,har ma tana kalubalantar kokarin da turawan yamma suke yi alokacin mai tsawo na nuna cewa Addini da siyasa ba su dace da ci gaban Iran ba, don haka mafiya na yammacin turai da sauran masu ji karfi kamar Isra’ila da yan jari hujja da Amurka suke fusata game da wanan ci gaban, shi yasa kullum suke mafarkin kai wa iran Hari.