Jaridar Haaretz ta bayyana a cikin wani rahoto cewa: A wancan lokaci sojojin Isra’ila sun yi ikirarin cewa an kashe wadannan yara ne sakamakon fadowar makamin roka na Saraya al-Quds (reshen soja na kungiyar Jihad Islami) a yankin Jabalia.
Iyalan yaran biyar kuma sun jaddada wajibcin gurfanar da firayi ministan Isra’ila kan wannan laifi a gaban kotun duniya, kasantuwar shi ne keda hannu kai tsaye wajen kai hare-haren.
A yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a wurin janazar kananan yaran a sansanin Jabalia, iyalai da suka rasa rayukansu sun bukaci hukumar Palasdinawa da ta dauki nauyin shigar da wanan kara kan kisan kananan yara da Isra’ila ta yi.
Haka nan kuma iyalan wadannan yara sun yi Allawadai da yadda gwamnatocin kasashen larabawa suka yi gum da bakunansu kan wannan mummunar ta’asa da Isra’ila ta aikata, da kuma yadda wasunsu ma suke ta hankoron ganin sun kulla hulda da Isra’ila a cikin irin wannan yanayi.
A rahoton da jaridar Arab Post ta bayar, ofishin Yair Lapid, firaministan gwamnatin yahudawan Sahayoniya, ya sanar a cikin wata sanarwa cewa, Isra’ila da Turkiyya sun yanke shawarar dawo da huldar jakadanci gaba daya da kuma musayar jakadu.
A cikin wannan bayani an bayyana cewa: Ci gaban dangantakar zai taimaka wajen zurfafa huldar da ke tsakanin bangarorin biyu, a bangaren tattalin arziki, kasuwanci da al’adu.
A wani bangare na bayanin ofishin firaministan gwamnatin yahudawan sahyoniya ya bayyana cewa: Bayan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin firaministan Isra’ila Yair Lapid da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Isra’ila da Turkiyya sun yanke shawarar mayar da jakadunsu a ofisoshin jakadancinsu domin ci gaba da hulda.
Kamfanin dillancin labaran Anatoliya ya habarta cewa, a nasa tsokaci na farko kan sanarwar da Isra’ila ta yi na musayar jakadu da Ankara, ministan harkokin wajen Turkiyya ya yi ikirarin cewa: “Za mu ci gaba da kare hakkin Falasdinu.”
Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Çavuşoğlu ya kuma bayyana cewa, Isra’ila da Turkiyya za su tura jakadu, wani muhimmin mataki a yunkurin da bangarorin biyu ke yi na daidaita alaka.
Shi ma shugaban gwamnatin yahudawan Isaac Herzog ya rubuta a shafinsa na Tuwita game da haka: inda ya ce; na yaba da sake dawo da cikakkiyar huldar jakadanci tsakanin Isra’ila da Turkiyya.
Wannan wani muhimmin ci gaba ne da muka jagoranta a cikin shekarar da ta gabata kuma zai taimaka wajen samar da karin dangantakar tattalin arziki, yawon bude ido da abokantaka tsakanin Isra’ila da Turkiyya.
Source: IQNA