Ivory Coast Na Karbar Taron Duniya Na COP-15 Kan Kare Muhalli.
Yau Litini ake bude taron Majalisar Dinkin Duniya kan kare muhalli.
Taron zai hada shugabannin kasashen duniya da masu ruwa da tsaki kan yadda za a magance matsalar kwararowar hamada da fari da zabtarwar kasa da sauran matsalolin muhalli.
Daga cikin shugabannin kasashen Afrika dake halartar taron, na Abidjan har da na NIjar Mohamed Bazoum, da takwaransa na Congo Félix Tshisekedi da na Togo Faure Gnassingbé, sai kuma Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya da zasu hadu da takwaransu na Ivory Coast Alassane Ouattara.
Ana sa ran kuma shugaba Emmanuel Macron na faransa, da kuma shugabar kwamitin kungiyar tarayyar turai Ursula von der Leyen, zasu halarci taron ta kafar bidiyo.
Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da MDD, ta bayyana cewa kashi 41% na kasa ya lalace, inda a ko wacce shekara ake hasarar heka miliyan 12 na kasa wanda ya kai fadin kasa kamar Benin ko Belgium.
READ MORE : Ganduje Ya Zabi Mataimakin Sa Nasir Gawuna A Matsayin Wanda Zai Gaje Shi.
Tsawon kwanaki goma masu tattaunawa daga kasashe 196 na duniya, zasuyi kokarin cimma matsaya ta bai daya kan yadda za’a yaki lalacewar kasa a cikin shekaru goma masu zuwa.