Israi’la Za ta Rusa Gidajen Falasdinawa 2 Da Ake Zargi Da Kai Hari A Garin Areial.
Sojojin Isra’ila sun dauki matakin rusa gidajen wasu falasdinawa matasa guda biyu da ake zargi da hannu wajen hari da aka kai kan wasu yahudawa masu gadi a Arewacin yankunan da isra’ila ta mamaye dake gabar yammacin kogin Jodan.
A cikin wata takarda da suka fitar a jiya Asabar sojojin Isra’ila sun bayyana cewa sun sanarwa da iyalan falasdinawan nan guda biyu Yousif Assi da kuma Yahya Mari da ake zargi da kai hari aniyarsu na rusa gidajensu , A ranar 29 ga watan Aprilu ne wasu masu dauke da makami suka harbe wasu masu gadi yahudawa guda biyu a kofar shiga wasu rukunin gidajen yahudawa da ke Ariel a arewa masu tsakiyar gabar yammacin kogin jodan
Sojojin Isra’ila sun kaddamar da samame da binciken kwakwafa na ganin sun gano wadanda suka kai harin inda bayan yan sa’oi suka sanar da kama wadanda ake zargin , inda aka ma daya a kauyen Qarawat bani Hassan a Arewa masu yamamcin garin na Areial.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun soki Isra’ila game da ci gaba da rusa gidajen falasdinawa da ake zargi suna da hannu wajen kai hari ,dubban falasdinawa ne aka kora daga gidajen su duk da yake cewa ba’a arginsu da aikata laifin komai ba, saboda bakar siyasar mamaya da gwamnatin sahyuniya ke aiwatarwa tun a shekara ta 1967.