Isra’ila Tana Shirin Rusa Gidan Wani Fursinan Siyasa A Yammacin Jenin.
Wata majiyar radiyon yahudawan Isra’ila ‘yan mamaya bada sanarwan cewa gwamnatin HKI tana shirin rusa gidan falasdinawa 2 Umar da Ghaith Jarradat dake kudancin birnin Jenin.
Labarin ya kara da cewa a jiya ma sojojin yahudawan sun nufi unguwar Silatul-Harithiyya da ke yamma da garin Janin, amma mayakan saraya Qus sun tilasta masu komawa baya. Sojojin HKI sun kama Ghaith da shakikinsa Umar ‘yan shekara 21 a duniya ne da kawunsu sheikh Muhammad Yusuf Jarradat a wani sumame da suka kaiwa yankinsu silsilatul Harithiyya kimani watan guda kenan, tare da zargin suna da hannu a wani harin da mayakan sara quds sukakaimasu.
READ MORE : Wasu Sojojin Isra’ila Biyu Sun Jikkata Bayan Kai Musu Harin Ramuwar Gayya.