Isra’ila ta harba makamin da ya yi kaca-kaca da gidan jagoran kungiyar Hamas a zirin Gaza.
Har yanzu ba a tantance adadin mutanen da rugujewar gidan ya yi sanadiyyar mutuwarsu ba.
Rikici tsakanin yahudawa da Falasdinu na ci gaba kamari, an yi asarar rayuka da dama a yankin Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare kan sassa daban daban na zirin gaza, ciki har da makamin rokar da ta harba kan gidan babban jagoran kungiyar Hamas Yehya Al Sinwar, BBC ta rahoto.
Babu tabbaci kan adadin mutanen da aka kashe ko suka ji raunuka a hare-haren da aka shafe kwana bakwai yahudawa da Hamas na kai wa juna hari, kungiyar Hamas ta mayar da martani ta hanyar harba rokoki da dama zuwa wasu biranen Isra’ila a wani mataki na ramuwar gayya bayan kai musu hari da yahudawan sukayi.
Jami’an lafiya a zirin Gaza sun tabbatar da cewa kusan mutane 150 sun mutu a hare-haren da aka shafe mako guda ana yi, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane 10 a a kasar ta yahudawa..
Hare-hare a yankin na kara ta’azzara, an yi asarar rayuka da dama ciki har da mata da kananan yara.
Isra’ila da Falasdinu sun shafe shekaru suna zaman doya da manja, inda suka kasance suna kai juna hare-hare, lamarin da ya jawo mutuwar dubban dubatan mutane cikin shekaru.
A wani labarin, Dubun-dubatar masu zanga-zanga sun yi jerin gwano zuwa ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Landan don kira ga daukar matakin gaggawa daga gwamnati don kawo karshen mummunan muzgunawa da ake yi wa Falasdinawa a rikicin Gaza.
Rikicin na Gaza ya tilasta wa dubban Falasdinawa barin gidajensu saboda yawan asarar rayuka da dukiyoyi.
Jaridar Punch a baya ta ba da rahoton cewa Shugaba Recep Erdogan na Turkiyya ya yi kira ga Shugaban, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), da ya ba da hadin kai ga Falasdinawa bayan sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai wa Kudus da Gaza.