Kungiyar kare hakkin fursinoni ta falasdinu wacce aka fi sani da (PPS) ta bayyana cewa daga shekarar 2015 zuwa 2022 haramtacciya kasar isra’ila ta tsare fiye da kananan yara 9000.
A wani rahoto da kungiyar ta fitar ta bayyana cewa daga cikin masu kananan shekaru 19000 da isra’ilan ta kama a kwai wadanda suke kasa da shekaru 10, wadanda suke cikin wadanda aka kama kuma aka garkame tun bayyanar intifada a saftambar 2000.
Kungiyar ta kuma tabbatar da cewa ko a halin da ake ciki yanzu ma isra’ilan ta kuma kama kananan yaran falasdinawa 160 kuma tana tsare da su.
Kamar yadda kungiyar PPS din ta tabbatar tace a sakamakon tattaunawa da wasu yaran da suk kubuto daga hannun jami’an haramtacciyar kasar isra’ilan ta tabbatar da cewa, duk yaran da isra’ilan take kamawa sukan fuskanci azabtarwa ta janibobin jiki da kuma abinda ya shafi hankulan su a hannun jam’ian taron haramtacciyar kasar isra’ila, wadanda kanyi amfani da injunan da ke zama barazana ga ‘yancin yaran.
Wannan jawabin na PPS yana zuwa ne a dai dai lokacin da ake bikin zagayowar ranar yara ta falasdinu wacce ke zaman ranar 5 ga watan afrilu.
A satumbar 2021 cibiyar dake kokarin tallafawa fursinoni dorawa kan karatukan su ta bayyana cewa, isra’ila tayi kokarin dakushe kokarin yaran falasdinawa daga neman ‘yancin kasar su ta hanyar kama su da kuma amfani da hanyoyin azabtarwa da kuma kokarin tsayar musu da karaun su wanda hakan ke zaman babban matakin tauye hakkin dan adam.
Rahotanni mabambanta daga yankunan falasdinu sun tabbatar da cewa shigowar wata mai alfarma sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun tsananta hare hare kan falasdinawa wanda duniya ke kallon hakan a matsayin babban zalunci gami da tauye hakkin raunanan falasdinawaa wata mainalfarma wanda musulmin duniya ke gabatar da ibadar azumi.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun bayyana cewa ayyukan isra’ila ya sabawa dan adamtaka kuma babbar barazana ce ga ‘yancin ‘yan adam.