Isra’ila ta ce makaman roka akalla dubu 1 da 500 mayakan Falasdinawa suka harba cikin kasar a cigaba da fadan da suke gwabzawa biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin bangarorin biyu a birnin Kudus a karshen makon da ya gabata.
Rikicin tsakanin Isra’ila da Falasdinawa dai na cigaba da yin muni musamman a jiya Laraba, duka da kiraye-kirayen hukumomin kasa da kasa kan kawo karshensa.
A ranar Laraba dai hotunan bidiyon dake yawo a kafafe daban daban sun nuna yadda luguden wutar da jiragen yakin Isra’ila ke yi kan Falasdinawa a birnin Gaza yayi sanadin rushewar wani kafataren gini mai benaye da dama da ya kunshi ofisohin kafafen yada labarai.
Wani yankin birnin Gaza da jiragen yakin Isra’ila suka yiwa luguden wuta.
Wani yankin birnin Gaza da jiragen yakin Isra’ila suka yiwa luguden wuta. AP – Adel Hana
Kawo yanzu Falasdinawa akalla 69 aka tabbatar da mutuwarsu ciki har da yara 17, yayin da wasu sama da 300 suka jikkata.
Farmakin Isra’ilar dai ya biyo bayan makaman rokar da mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas ke harbawa cikin kasar tun a ranar Litinin inda suka halaka mutane 6, bayan karewar wa’adin da Hamas din ta dibarwa Isra’ila kan janye jami’an tsaronta daga Masallacin Al Aqsa, inda suka ci zarafin fararen hula a yayin da suka ibada.
Tashin hankalin baya bayan nan dai ya samo asali ne kan tilasta korar wasu Falasdinawa daga wata unguwa mai suna Shiekh Jarrah, yankin da falasdinawa da Isra’ila suka dade suna shari’a kan hakkin mallakarsa tun shekarar 1972.
Amurka ta nuna goyon baya ga shirin Majalisar Dinkin Duniya na gudanar da zama na musamman kan rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da yankin Falasdinu, dai dai lokacin da jami’an diflomasiyya ke ganin Washington ce ta yi karfa karfa wajen hana taron a gobe Juma’a.
Sakataren wajen Amurkan Antony Blinken ya bayyana cewa kasar na goyon bayan taron kwamitin tsaro na Majalisar, sai dai zuwa makon gobe za a iya samun damar tunkarar rikicin ta fuskar Diflomasiyya gabanin hukuncin Majalisar.
A wata zantawarsa da manema labarai, Blinken ya jaddada aniyar Amurka ta tabbatar da zaman lafiyan gabas ta tsakiya.
Zuwa yammacin yau Alhamis Falasdinawa 300 Sojin Isra’ila suka kashe a rikicin yayinda wasu daruruwa kuma suka sake jikkata kari kan wadanda ke raunata kowacce rana tun bayan farowar rikicin kwanaki 6 da suka gabata.
Sojin Saman Isra’ila ne ke ci gaba da amfani da jiragen yaki wajen kaddamar da farmaki kan Falasdinawan bisa fakewa da yakar Sojin Hamas kungiyar da ke rike da makami a yankin.