Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 10 a luguden wuta kan Zirin Gaza.
Mutum aƙalla 10 Isra’ila ta kashe a hare-hare ta sama da ta kai kan Zirin Gaza, cikinsu har da kwamandan gwagwarmaya na Falasɗinawa a ranar Juma’a.
Hukumomin lafiya a yankin sun ce cikin waɗanda aka kashe akwai ƙaramar yarinya da kuma raunata wasu gommai.
Firaministan Isra’ila ya ce an kai harin ne bayan samun “barazanar gaggawa” daga ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad (PIJ) sakamakon kama ɗaya daga cikin mambobinta a farkon makon nan.
PIJ ta harba makaman roka fiye da 100 “a martanin farko da ta mayar”, in ji shi.
READ MORE : Kashe mutum 10 da Isra’ila ta yi a Gaza ya harzuƙa Falasɗinawa.
Rundunar sojan Isra’ila ta ce hakan ne ya sa ta fara luguden wuta a yammacin Juma’a ta hanyar kai wa sansanin ‘yan gwagwarmayar hari.
READ MORE : Taiwan: Ziyarar Nansi Pelosi Ta Bar Baya Da Kura A Yankin Asiy.
READ MORE : Amurka ta ce akwai yiwuwar China za ta kai wa Taiwan hari.
READ MORE : Amurka ta sanar da kashe shugaban Al-Qaeda Ayman al-Zawahiri a Afghanistan.
READ MORE : Yarima Charles Na Ingila Ya Karbi Rashawa Daga Iyalan Osama Bin Laden.
READ MORE : NDLEA ta ƙwace ƙwayar Tramadol guda miliyan 2.7 a Legas.