Rahotanni daga zirin gaza na tabbatar da cewa a ranar litinin sojojin haramtacciyar kasar isra’ila sun kai wani harin ba sani ba sabo kan sansanonin ‘yan gwagwarmaya a yankin gaza.
Harin wanda aka kaishi ta hanyar amfani da jirage masu saukar ungulu gami da manyan rokoki, kamfanin yada labaran falasdin na shehab ya rawaito cewa a kai harin ne a kudancin gaza zuwa gabashin birnin Rafah.
Rahotanni sun tabbatar da cewa isra’ila ta kai tagwayen hare hare a yankunan inda tayi ikirarin cewa, ta kai harin ne domin mayar da martani kan wasu rokoki da tace an harba zuwa bangaren haramtacciyar Isra’ilan.
Rahotanni daga bangaren falasdinu sun tabbatar da cewa hare haren wadanda aka kai sun jawo kararrakin fashewar bama bamai kuma hakan ya sabbaba dauke wutar lantarki a yankunan da abin ya shafa.
Jim kadan bayan hakan jiragen yakin haramtacciyar kasar isra’ila masu kirar UAVs sun soma sintiri sararin samaniyar yankin domin sanya tsoro a zukatan fararen hula mazauna yankin.
Hakanan jiragen yakin isra’ila sun kuma kai hari a arewacin yankin yankinnna zirin gaza.
‘Yan gwagwaramayar falasdinawa dai sun dinga daukan matakan kare kai da na’urorin kakkabe makaman da ake harbawa.
Gwamnatin haramtacciyar isra’ila dai ta dingi bada dalilai marasa tushe balle makama a sabbin hare haren da take aiwatarwa a kan falasdinawa, wanda hakan ta bayyana tana so ne ta sanya yankin gazan cikin wani mawuyacin yanayi sa’annan da tsorata mazauna yankin wadanda basu ji ba basu gani ba.
Ba sabon abu bane ba dai irin wadannan hare haren ta’addanci da sojojin haramtacciyar kasar ta isra’ila suke kaiwa a kan mazauna yankin na zirin gaza dama falasdinu baki daya amma babu matakin da ake iya dauka a kan yahudawan sahayoniyan, sai dai ayi surutai a kafafen yada labarai a wuce wajen, ita kuma isra’ilan ta cigaba da aiwwtar da ta’addancin ta a kan raunanan larabawa musulmai.