Isra’ila Ta Kai Hari Da Makami Mai Linzami A Filin Jirgin Sama Na Aleppo Da Ke Siriya.
A yan shekarun baya bayan nan rahotanni sun bayyana irin yadda gwamnatin yahudawa sahyuniya take ci gaba da keta hurumin kasar Siriya inda ta kaddamar da hare-hare a birnin damaskas da ma sassa daban –daban na kasar, sai dai wanna wuce gona da irin na cin karo da makaman kariya na kasar ta siriya.
Rahoton da kamfanin dillancin labarai na SANA ya nakalto ya nuna cewa a daren jiya ne filin zirga zirgan jiragen sama na Aleppo ya fuskanta harin makami mai linzami daga HKI, kuma shi ne hari na 2 da ta kai tun a makon jiya, rahoton yace naurar tsaron sararin samaniya na kasar Siriya ya kakabo makamin da isra’ila ta harba ,
Dakarun sojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya dake da sansani a kasar Labanon sun bayyana cewa gwamnatin Isra’ila tana keta kudurin majalisar dinkin duniya a kallum rana , da kuma hurmin sararin samaniyar kaar Labanon.
Minsitan harkokin wajen kasar siriya ya fitar da wani bayani a baya bayan nan inda yayi tir da harin da Isra’ila take kai a kasar siriya, yace Damaskas za ta yi amfani da hakokin da doka ta bata wajen mayar da martani da ya dace game da wuce gona da irin Isra’ila.