Isra’ila Ce Silan Duk Wani Rikici A Gabas Ta Tsakiya Inji MDD.
Wani rahoto da kwamitin bincike da hukumar kare hakkin dan adam ta MDD, ta fitar ya nuna cewa Isra’ila ce silan duk wani rikici dake faruwa a yankin.
‘’Mamayar da Isra’ile ke wa Faladinu da kuma nuna wa al’ummar falasdinu wariya su ne Ummul-Aba’isin duk wani rikici dake faruwa a yankin, inji rahoton na MDD.
Kawo karshen mamayar yankunan da Isra’ila ke yi, da kuma bin dokokin da kwamitin tsaron MDD, ya shata su ne kawai zasu iya kawo karshen rikice rikicen dake faruwa a yankin a cewar shugabar kwamitin Navi Pillay.
A bara ne aka kafa kwamitin binciken bayan yakin kwanaki 11 da ya barke tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas, inda a watan Mayu 2021, falasdinawa 260 suka mutu yayin farmakin Isra’ila kan Gaza, sai kuma ‘yan Isra’ila 11 da suka mutu sakamakon harbin rokokin ‘yan Hamas.
READ MORE : MJTF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da Dari Takwas A Tafkin Chadi.
Saidai tuni Isra’ila ta yi fatali da rahoton binciken tana mai zargin shugabar kwamitin da cewa daya ce daga cikin ‘yan kin jinin Isra’ila.
READ MORE : Iran Za Ta Iya Sauya Matsayarta Dangane da Hadin Kan da Take Baiwa IAEA.