Kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin ta’addancin da aka kai kan mahalarta bikin tunawa da shahidan Suleimani
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: kungiyar ta’addanci ta Da’ish ta dauki alhakin harin ta’addancin da aka kai shekaran jiya laraba kan mahalarta bikin tunawa da shahidan Suleimani a Golzar Shahadai na Kerman, ta hanyar buga wata sanarwa.
A cewar wata sanarwa da wannan kungiyar ta’addancin ta wallafa a tashoshinta na Telegram, wasu ‘yan kunar bakin wake 2 ne suka tayar da bama-baman na shekaran jiya.
Kungiyar ISIS ta yi ikirarin cewa “Umar Al-Muhed” da “Saifullah Al-Mujahid” sune ‘yan kunar bakin wake biyu da suka yi sanadin shahadarsu ta hanyar tayar da bama-bamai a tsakanin mutanen garin Kerman.
Wasu fashe-fashen bom na ‘yan ta’adda guda biyu a yammacin Laraba a kan hanyar Golzar Shahadai da ke Kerman, sun yi sanadin shahidai 84 ko 94 ko ma sama da 100 kamar yadda wasu rahotonni suka kawo, yayin da wasu 284 suka jikkata, lamarin da ya janyo Allah-wadai daga kasashe da kungiyoyi daban-daban.
Bayan wadannan fashe-fashe da kuma shahadar al’ummar Iran da dama, kasashen duniya da dama sun aike da sakonnin yin Allah wadai da wadannan hare-hare tare da nuna juyayinsu ga iyalan wadanda abin ya shafa da kuma gwamnati da al’ummar Iran.
Source: ABNAHAUSA