IRGC, Ta Sanar Da Kai Jerin Hare hare Kan Cibiyoyin Leken Asirin Isra’ila A Erbil.
Dakarun kare juyin juya halin musulinci na Iran, sun tabbatar da kai hare hare da makamai masu linzami kan wasu sansanonin leken asirin Isra’ila a Erbil.
Harin dai a cewar IRGC, martani ne kan wani harin da Isra’ilar ta kai a kusa da birnin birnin Damascos na Siriya ranar Talata wanda a yayinsa wasu kwamandojinta biyu sukayi shahada.
Sanarwar IRGCn, ta ce daga yanzu ba zata taba saurara wa wata tsokana ko irin wannan danyan aikin da Isra’ila ke aikatawa ba.
READ MORE : Da Zarar Amukra Ta Amince, Za A Kulla Yarjejeniyar Nukiliya.
Makamai masu linzami 12 ne dai Iran ta harba kan sansanonin leken asirin Isra’ilar a birnin Erbil na Iraqi.