Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) ya yaba da karfin soja da manyan makamai na kasar, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta zarce manyan kasashen duniya a fannin fasahar tsaron sararin samaniya.
Da yake jawabi a wani biki a ranar Talata, Kwamandan na rundunar IRGC Manjo Janar Hossein Salami ya yaba da gagarumin ci gaban da Iran ta samu a fasahar soji ta zamani da kuma yadda kasar ke dogaro da kanta wajen kera nagartattun kayan aikin soji, duk kuwa da takunkumin da aka sanya mata.
“Muna matsayi na farko a fagen fasaha mai yawa, Hatta a fagen tsaron sama, mun zarce manyan kasashen duniya ta yadda wasu kasashe ke sayen makamanmu,” in ji Salami.
A wani labarin na daban manyan jagororin siyasa na kasar Iraki, sun cimma matsaya game da komawa teburin sulhu, domin warware rigingimun dake addabar kasar.
An cimma wannan msataya ce yayin zaman da sassan masu ruwa da tsaki a siyasar kasar suka gudanar.
Wata sanarwa da ofishin riko na firaministan kasar Mustafa al-Kadhimi ya fitar, ta ce yayin zaman wanda shugaban kasar Iraki Barham Salih, da kakakin majalissar dokokin kasar, da wakiliyar musamman ta babban magatakardar MDD a kasar, da sauran jiga-jigan jam’iyyun siyasar kasar suka halarta, an amince a kafa wata tawaga mai wakilcin jam’iyyun siyasa daban daban, wadda za ta tsara dabarun gaggauta gudanar da sahihin zabe, da sake nazarin dokar zabe, da sake inganta hukumar zaben kasar.
Har ila yau, sanarwar ta jaddada bukatar yin gyaran fuska ga tsarin siyasar kasar Iraki, ta hanyar kafa dokoki masu alaka, da tsare-tsaren ayyukan hukuma, bisa tanadin kundin tsarin mulki a dukkanin matakai da za a aiwatar.
Source: ABNAHAUSA