Iraqi Ta Kira Jakadanta A Sweden Bayan Kona Al Kur’ani A Kasar.
Kasar Iraqi ta sanar da kiran jakadanta a Sweden a wani mataki na nuna bacin rai gameda kona Al Kur’ani mai tsarki a kasar.
A Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Irakin ta fitar, ta ce kona Al Kur’ani wani lamari ne mai daci a alakar Sweden da al’ummar musulmi duniya.
Iran ma ta kira mai kula da harkokin kasar Sweden a Tehran domin nuna bacin ranta kan lamarin.
kasar Iran ta ya yi Allah wadai da lamarin na wulakanta Al’kur’ani mai tsarki a kasar ta Sweden.
Saeed Khatibzadeh ya sanar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya da masu tsattsauran ra’ayin da suka cinnawa Al kur’ani mai tsarki wuta a birnin Linköping na kasar Sweden da sunan ‘yancin fadin albarkacin baki.
Khatibzadeh ya ce wannan cin mutuncin da aka yi a cikin watan Ramadan ya sanya al’ummar Musulmi cikin bacin rai da kuma fusata a duk fadin duniya.
Ya kuma bukaci gwamnatin Sweden za ta dauki mataki mai karfi cikin gaggawa kan wannan ta’addanci domin kada irin wannan lamari ya sake faruwa.
An shafe kwana uku ana zanga-zanga a Sweden kan adawa da masu tsauttsauran ra’ayi da ke kyamar baki da suka kona Al Kur’ani bayan gangamin shugaban jam’iyyar masu kyamar musulmi Rasmus Paludan.