Iraqi; Magoya Bayan Muqtada Assadr Sun Mamaye Majalisar Dokoki Don Bayyana Korafinsu.
Daruruwan magoya bayan Muqtada Assadr a kasar Iran sun mamaye majalisar dokokin kasar wanda yake cikin yankin “Green Zone” na birnin Bagdaza a jiya Laraba don gabatar da korafinsu kan yadda majalisar take son dora wani wanda basa so a matsayin firai ministan kasar.
Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayyana cewa babu wani dan majalisar a cikin ginin majalisar a lokacinda magoya bayan Assadr suka shiga cikin majalisar. Labarin ya kara da cewa masu tarzoman sun sami masu gadi ne kawai a cikin majalisar wadanda suka bude masu majalisar ba tare da wata turjiya ba.
Firai ministan kasar Iraqi Mustafa Alkazimi ya bukaci magoya bayan malamin su fice daga cikin majalisar su kuma fice daga yankin Green Zone| don yanke ne wanda yake dauke da ofisoshin jakadancin kasashen duniya da dama da kuma gine-ginen gwamnatin kasar ta Iraqi.
READ MORE : Tattaunawar Makamin Nukilya: Iran Tana Maraba Da Hanyoyin Diflomasiyya.
Gungun jam’iyun Sadar dai sun sami rinjaye a majalisar dokokin kasar a zaben watan Octoban da ya gabata, amma kuma sun kasa kafa gwamnati duk tare da rinjayen da suke da shi a majalisar.
READ MORE : Iran Da Gaske Take Tana Bukatar Yarjeniya Mai Karfi Dangane Da Dage Mata Takunkuman Tattalin Arziki.