Iraqi; Dakarun Hashdu Sun Wargaza Shirin Daesh Na Hare-Hare A Kasar.
Majiyar dakarun Hashdu Ashabi na kasar Iraqi ta bada sanarwan cewa dakarun sun sami nasara wargaza wani shirin kungiyar yan da’atta ta Daesh na kashe mutane a lardin Samira.
Kamfanin dillancin labaran ‘Bagadadul Yaum’ ya nakalto majiyar dakarun na cewa sun kwace wasu boma-bomai wadanda mayakan kungiyar Daesh suna dana a yankin ‘Sayyid Garib’ kusa da birnin Samira wadanda suke nufin kashe mutanen yankin da su.
Hare-haren mayakan kungiyar Deash a kasar a cikin ‘yan watannin da suka gabata ya kara yawa, kuma mafi yawan mutanen kasar Iraqi suna ganin gwamnatin Amurka ce take goyon bayan yan ta’adda don ta ci gaba da wanzar da sojojinta a kasar ta Iraqi.
READ MORE : Lebanon; Mutanen Kasar Sun Yi Zanga-Zangar Yin Allawadai da Kokarin Isra’ila Na Satar Man Kasar.
Tun shekara ta 2020 ne majalisar dokokin kasar Iraqi ta bukaci ficewar sojojin kasashen waje, musamman na Amurka daga kasar amma gwamnatin Amurka ta ki hakan.
READ MORE : Wasu Kungiyoyi A Sudan Sun Ki Halattar Zaman Sulhuntawa.
READ MORE : Jakadan Rasha; Ya kamata Isra’ila ta daina munanan ayyukan da take yi wa Siriya.
READ MORE : FM Nigeria yayi kira da a hada kan musulmi akan takfiriyya.