Iran; Za’a Iya Kulla Yarjejeniya Idan Amurka Ta Dawo Cikin Jarjejeniyar Da Aka Cimma.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdollahiyan ya fadi cewa za’a iya farfado da yarjejeniyar JCPOA da aka cimma matsaya a kai,idan America ta dawo da yin aiki da yarjejeniyar da aka cimma matsaya a kai
A shekara ta 2015 ne aka kulla yarjejeniyar nukiliya JCPOA tsakanin kasashen Rasha, china, birtaniya, faransa da kuma kasar Amurka sai dai a ranar 18 ga watan mayun shekara ta 2018 America ta yi fatali da yarjejeniyar kuma ta sake kakabawa sabbin takunkumi kan kasar Iran.
An fara tattaunawa zagaye na 8 a birnin viyanna a ranar 27 ga watan Disemba kuma yana ci gana da gudana bayan da aka she hutun takaitaccen lokaci sai dai babu kasar America a ciki.
Da yake ishara game da ziyarar da Entique Moran a iran minsitan harkokin wajen turai Josep Borrel ya fadi a gaban taron kungiyar G-7 cewa ya yaba sosai game da tattaunawarsa a Tehran,
READ MORE : Abin da ya sa na janye daga takarar shugaban kasa bayan an tara min kuɗaɗe – Adamu Garba.
Anata bangaren kasar iran ta bayyana cewa matukar ana son a cimma matsaya a yarjejniyar dole ne America ta dawo cikin tattaunawar ta hanyar cire mata dukkan takunkumin da ta kaka ba mata,