Kafar sadarwa ta Leadsership Hausa ta rawaito cewa, ‘Yan sanda a kasar Iran sun sanar da c da fara amfani da fasahar zamani a wuraren taruwar jamIa’a domin ganowa gami da hukunta matan da basa sanya hijabi.
Wata sanarwa ta tabbatar da cewa, an shirya tsaf domin amfani da hanyoyin zamani na cigaba domin wannan aiki.
Sanawar tace daga cikin matakan da za’a dauka har da amfani da kyamarori wadanda zau dauki hoton masu karya dakar sanya hijabin.
Za’a rika aikewa da masu take dokar sakaonnin gargadi na cewa za’a iya daukar matakin shari’a a kansu matukar suka cigaba da halin take dokar ta sanya hujabi.
An gano adadin karye dokar sanya hijabi a kasar Iran ya karu tun bayan lafawar wata zanga zanga da akayi a wasu garuruwan kasar a watannin baya sakamakon mutuwar wata mata a hannun ‘yan sandan hisba.
Matar mai suna Mahsa Amini an zarge ta da laifin karya dokar sanya hijabi inda ‘yan sanda suka kama ta amma daga baya ta rasa rayuwar ta bisa dalilan rashin lafiya da take fama da shi.
Sai dai kafafen yadda labarai mallakin kasashen yamma sun zargi ‘yan sandan Iran da alhakin mutuwar wannan mata, zargin da ‘yan sandan suka musanta tare da kafa hujja da bayanan likitoci da suke nuna dama matar tana fama da rashin lafiya kuma dalilin mutuwar ta kenan.