Iran Za Ta Iya Sauya Matsayarta Dangane da Hadin Kan da Take Baiwa IAEA.
Wani mamba a kwamitin tsaron kasa da manufofin ketare na majalisar dokokin Iran ya sanar da gudanar da taron gaggawa na wannan kwamiti dangane da taron na majalisar manyan alkalan hukumar IAEA.
Fadahossein Maleki, mamban kwamitin tsaro na kasa da harkokin waje na majalisar shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa, za a gudanar da taron gaggawa na wannan kwamiti dangane da taron kwamitin alkallai na hukumar IAEA, a yammacin yau Laraba, a hedkwatar kwamitin tsaro na majalisar dokokin kasar da kuma halartar jami’ai daga hukumar makamashin nukiliya da ma’aikatar harkokin waje.
Ya ci gaba da cewa, “A cikin wannan taro, za a tattauna bayanan baya-bayan nan da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya yi kan shirin nukiliyar Iran da kuma yunkurin da kasashen Turai uku suka yi a taron kwata-kwata na kwamitin gwamnoni kan Iran.”
Shugaban kwamitin tsaron kasa da manufofin harkokin waje na majalisar dokokin kasar Iran ya fada a jiya Talata cewa, idan har hukumar ta IAEA ta yanke shawara, za mu sake duba batun tattaunawar nukiliyar, da kuma hadin kan da Iran take baiwa hukumar ta IAEA.