Iran Za ta Ci Gaba Da Rike Kyamarorin Hukumar Nukiliya Har Sai An Rattaba Hannu.
Kakakin hukumar nukiliya ta kasar Iran Behrouz Kamalvandi Jaddada cewa za’a ci gaba da ajiye dukkan bayanai da suka shafi cibiyoyin nukiliyarta har sai an sanya hannun kan yarjejeniyar nukiliya tsakaninsu.
Da yake bayani a wata hira da yayi da tashar talabijin din Al’alam ta kasar iran game da batun sauya wasu Naurori wurin zama daga Karaj zuwa Natanz ya fadi cewa saboda ayyukan ta’adanci da aka yi kan tsai karaj yasa dole a dauki mataken tsaro masu tsauri yasa aka matsar da muhimman banharorin wadanan naurorin zuwa Natanz da Isfahan
Har ila yau ya kara da cewa an matsar da manyan sassan injinan ne zuwa wuri mafi aminci saboda muhimmancin da suke da shi amma har yanzu suna aiki.
Yace tuni aka aike da rahotanni zuwa ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya a matakai guda biyu. Na farko lokacin da ake sauyawa naurorin wuri , na biyu kuma lokacin da ake sanya Kyamarori da suka fara aiki
Daga karshe ya nuna cewa bama tattaunawa akan abubuwan da suka shafi bangaren fasaha a halin yanzu , duk da yake akwai sauran wasu batutuwa kasan da suka rashi da ya kamata a warwaresu.