Iran Yarjejeniyar Da Bata Dagewa Iran Takunkuman Tattalin Arziki Mafi Tsaurin Ba Ba Karbebbe Bane.
Shugaban majalisar koli ta tsaron kasa Ali Shamkhani ya bayyana cewa duk wata fahintar juna a tattaunawar dagewa Iran takunkuman tattalin arziki wanda bai hada da dage mata al-amuran da suka takurawa tattalin arzikin kasa ba, to ba fahintar juna mai kyau bane.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Shamkhani yana fadar haka a shafinsa na Twitter. Ya kuma kara da cewa wadanda suke wakiltan Iran a tattaunawar Vienna zagaye na 8, suna da cikekkiyar masaniya kan abinda zasu tattauna a kansu.
Don haka takunkumanda su ne jigo a takurawa mafi muni a kan kasar Iran sanannu ne, kuma matukar ba’a dauke wadannan ba, ba inda za’a je.