Jamhuriyar musulunci ta Iran tayi maraba lale da matakin da gwamnatin yemen ta dauka na tsagaita wuta har na tsawon kwana uku a yakin da ake fafatawa tsakanin yemen din da kuma taron hadin gwuiwar sojoji karkashin jagrancin saudiyya.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran din Sa’eed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai ranar talata, inda ya bayyana hakan a matsayin wani alami da kyakykyawan fatan kawo karshen wannan dambarwa duba da yamanawan a matsayin wadanda aka fi zaluncta kuma sune aka iske har gida ake ta ma luguden wuta tsawon shekaru.
”Wannan shiri wanda gwamnatin yemen da gabatar cikin cikakken imani da kuma fatan kawo karshen dukkan matsaloli da kuma warware matsalolin siyasa da dillomasiyya abin yabawa ne” kamar yadda khadibzadeh ya bayyana.
Wannan tsagaita wuta na kwana uku na iya share hanyar samun sulhu gami da kawo karshen wanna yaki amma idan bangaren saudiyya da kawayen ta sun dauki lamarin da muhimmanci kuma sunyi abinda ya kamata, a ta bakin sa’aeed khadinzadeh.
Duba da yadda wata mai alfarma na ramadana ya gabato muna fata a samu canji daga yanayin da ake ciki ma’ana sa samu kwanciyar hankali gami da taimakon dan adamtaka ta hanyar ajje makami gami da kawo karshen matsaloli da kuma canjin fursinonin yaki daomin saukaka ma muaten da iyalan su a cikin wata mai alfarma na azumi.
A yammacin ranar lahadin da ta gababa ne dai shugaban majalisar samar maslahar yemen Mahdi al-Mashat ya sanar da matakin tsagaita wutar na kwana uku.
Amma sai dai yemen ta gargadi saudiyya kan cewa tayi amfani da wannan dama ta tsagaita wutar kwan uku yadda ya kamata domin samun maslaha da kuma fahimtar juna.
Shekaru fiye da bakwai ne dai sojojin saudiyya da gamayyar wasu sojojin haya ke ta faman kai hare hare kan fararen hula a yemen lamarin da yayi sanadin rasa rayukan fararen hula da dama.