Iran Tana Son Bunkasa Alakarta Da Kasashen Nahiyar Africa.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdullahiyan, ne ya bayyana cewa bunkasa alaka da kasashen nahiyar Africa yana daga cikin ginshikan siyasar waje ta Iran.
Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya tattauna ta wayar tarho da takawaransa na kasar Murtaniya, ya kuma jinjinawa kasar akan yadda take goyon alummar Falasdinu da suke fuskantar zaluncin ‘yan sahayoniya.
Har ila yau, ministan harkokin wajen na Iran ya kuma taya takwaran nasa murnar shigowar watan Ramadan mai alfarma tare da tabbatar da cewa Iran tana son bunkasa alakarta da Murtaniya.
Da yake Magana akan batutuwan da suka shafi halin da kasashen musulmi suke ciki, Amir Abdullahiyan ya ce; Jamhuriyar musulunci ta Iran tana son ganin an tsagaita wutar yaki akasar Yamen, tana kuma goyon bayan tattaunawa a tsakann al’ummar Yamen, da kuma kawo karshen killace kasar da aka yi.
READ MORE : Sojin Najeriya sun kashe Kwamandan IPOB a Imo.
A nashi gefen, ministan harkokin wajen kasar Murtaniya Wuld Marzuk ya yaba da alakar kasashen biyu tare da nuna fatan ganin an bunkasa ta. Haka nan kuma ya jaddada muhimmancin matsayar kasashen biyu dangane da Falasdinu.
READ MORE : Mali ta samu karin makaman soji daga Rasha.