Iran Tana Marhabin Da Yarjejeniya Da Za’a Iya Dogaro Da Ita A Tattaunawar Vienna
Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdallahiyan da yake zantawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Japan ya fadi cewa Iran ashirye take na ganin an cimma ingantacciyar yarjejeniya da za’a dogara da ita a tattaunawar da ake yi a vianna na ci re ta takunkumi
Anasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Japan Hayashi Yoshimas ya yi ishara game da irin ci gaban da za’a samu tsakanin kasashen baiyu a bangaren tattalin arziki idan aka cire abubuwan dake kawo cikas, kana ya gayyaci takwaransa na Iran daya kawo ziyara birnin Tokyo
Har ila ya Amir Abdallahiyan ya yaba game da aniyar kasar Japan na bada gudunmawa a tattaunawar da ake yi yi tsakanin iran da kasashen turai 5 a viyanna, kana ya jadadda matsayin iran na ganin an cimma ingantaciyar yarjejeniya da za’a dora da ita.
Tattaunawar tasu ta mayar da hankali kan hanyoyin da kasashen biyu za su yi aiki tare a bangarori daban daban,